1) Yesu Ɗan Allah, yau ka zo! Mu fa me za mu yi? Mala'iku na sama, ku taimake mu waƙa. Yanzu da asubahi, yanzu da asubahi. Alhamdu ga Allah har abada! 2) Ya Almasihu, yau ka zo! Mu fa me za mu yi? Mu durƙusa gabanka, mu yi maka sujada, Mu girmama sunanka, mu girmama sunanka. Alhamdu ga Allah har abada! 3) Yesu jariri, Mai Ceto, Mu ƴaƴanka mun zo, Mu ƙanƙananan yara mun kawo maka ranmu Mu sa maka albarka, mu sa maka albarka. Alhamdu ga Allah har abada! 4) Baitalahmi ne zuciyata, Ya Yesu, yau ka zo! Ya Ruhu, ina roƙo, ka kawo shi a wurina Ya zauna har abada, ya zauna har abada. Alhamdu ga Allah har abada!مجد عظيم 野地的花 பூரண அழகை விவரிக்க முடியா, பூரண அழகை 눈을 들어 주를 보라 ạ̉ʿntny 주께 감사하네 Дай мне сказать просто я не могу молчать 나는 주만 높이리 Свят си อยู่ในพระวิญญาณ
Song not available - connect to internet to try again?