Kullayaumin ka yi addu'a.
Duk ka roƙa Allah ya ji.
Ba ya ta da alkawari.
Ba kankanta a idonsa.
Buɗe zuciya a gabansa,
Yi addu'a, shi ne mai ji.
Kada Mugun ya yi nasara.
Yesu wanda an jarraba
Zai riƙe ka, ka yi addu'a.
Ko da ƙunci ya danne ka.
Ba ya kyale wahalarka,
Zai daidaita, ka yi addu'a.
Kwanciyar ranmu sai bangaskiya.
Allah shi ne mai amsawa,
Dole kullum mu yi addu'a.