1) Zo, mutane, rera waƙa, Cika sammai da yabo. Yabe shi, Mai Magani ne, Don ya ceci duniya. Makiyayi, Mai Cetonmu, Ana biyayya da shi. 2) Saboda cetonmu ne fa, Ya zo ya ba da jininsa, Ya yi aikin gafara ma, Ya mutu, mun huta ma. Tashinsa na ɗaukaka ne, Sarkin rai har abada. 3) Yanzu bisa kursiyinsa Girma, iko nasa ne. Ana rera, Halleluya, Waƙar ƴaƴan haske ce, Shi Sarki nc da Shugaba, Nasara duk tasa ce. 4) Ga giraya da algaita, Rera waƙar yabonsa. Duniya ma ki saurare mu, Sarkin rai ya rinjaya! Rago wanda aka kashe Ya rayu, ya tashi kuwa. 5) Yabo, ɗaukaka ga Uba, Yabo, ɗaukaka ga Ɗa, Yabo, ɗaukaka ga Ruhu, Uku cikin ɗaya ne. Makaɗaicin Allah namu Girma, yabo nasa ne.Hatak yoshoba moma Merak ediyorum Kami Menanti Kedatanganmu Ca si noi copiii Krv zvierat všetkých čias Viacej ako dobrý Priateľ Прошу Не Уходи ياللي حبيتني Hazme Un Instrumento Մեր Ելքն ես
Song not available - connect to internet to try again?