1) Ƙaunar Allah, ba kamarta Ko a Sama ko a nan, Sai ka cika mana zuciya, Sai mu zama cikakku. Yesu mai jin tausayinmu, Kai mai ƙaunar mutane, Ziyarce mu da cetonka, Shigo dukan zukata. 2) Sai ka huro mana Ruhu, Karfafa mu duk yanzu, Kai ne gādonmu, ya Allah, Za ka ba mu hutawa. Raba mu da son mugunta, Kai ne Ruhu, kai ne Rai, Farkon kome da cikarsa, Allah ne Madauwami. 3) Zo, ya Allah, domin ceto, Ba mu duk alherinka, Zo da sauri, zo da zama, Zauna nan har abada. Kai ne kullum mu ke yabo, Bautarka ce mu ke so, Yin addu'a da sujada Sun yi mana daɗi yau. 4) Mai da mu sabuwar halitta, Tsarkake mu duka fa Har mu ga fansa mai girma Wadda ka yi dominmu. Sāke mu da darajarka, Har mu isa Sama can. Za mu rusuna gabanka Muna maka godiya,Славный Сион благодатный Бийикледеги Раббий ṣlạẗ ạlrwḥ క్రొత్త యేడు మొదలు zūn róng cóng nǎ lǐ lái Ынанырыг Vznešený Halleluya Այնժամ Ես Կմիանամ ạ̉nạ mḥtạj lmsẗ
Song not available - connect to internet to try again?