1) An kafa birni dai, ba nan ya ke ba, Mulki madauwami, ba nan ya ke ba. Allah mai gininsa, masu zuwa, tsarkaka, Birni na Sama ne, ba nan ya ke ba. 2) Mu kama baƙi ne, can sai mu je. Bin Yesus mu ke yi, can sai mu je. Sai mu saki duniya nan. Sai mu tashi daga nan, Tashi zuwa ƙasar can, can sai mu je. 3) Ba sauran kuka fa har abada. Mutuwa ta ƙare can har abada. Sai murna za mu yi, Almasihu za mu ji. Bautarsa za mu yi har abada. 4) Je zuwa birnin nan, zo, zo mu je. Kada mu tsaya nan, zo zo mu je. Yesu ke kiranmu, Yesu yana jiranmu, Shi jagabanmu ne, zo zo mu je.ạnt ạlly̱ fdytny̱ Загалмай yạ yswʿy أبت Danalıq Сакин Олур Билирим Рабсин Jézus, köszöntlek องค์พระคริสต์ทรงนำทัพมุ่งไป Mi-e-atât de dor يعجز كلامي
Song not available - connect to internet to try again?