1) Yesu ya kira almajiransa sha biyu. Lokacin da yake komawa sama Ya ce, "Su tafi su yi bishara Har duniya duka ta sami ceto." KORUS Bishara Yesu Za mu yi, za mu yi Babu tsoro fargaba ba za mu yi ba. 2) Sai ku fara a cikin Urushalima, Har in aiko maku da mai taimako. Ruhu mai tsarkina za ya bida ku, Ga shi ina tare da ku a kulluyaumi. Korus 3) Sai ku fara daga Urushalima, Samariya har da Galili. Dukan ƙauyuka suna bukatar ceto. Sa'an nan har iyakar duniya. Korus 4) Ku ɗauki giciyen Yesu domin bishara, Gama duniya tana mutuwa. Idan mu kyale su za su hallaka, Alhakinsu yana rataye a wuyanmu. Korus 5) Wanda ya nace cikin aikin bishara. Za ya sami ladan aikinsa. Za ya sami rawani na rai, Za mu yi mulki tare da shi har abada. KorusAbide With Me Amin, Haleluya! ياما ناس أروم قربًا Магтан дуулъя جايلك Ликуй! Господь грядёт Сəнин үчүн мəн јашајырам قدوس В моїй душі, сумнів не підступає
Song not available - connect to internet to try again?