1) Ga mutum mai ƙazamin Ruhu Ya gamu da Yesu dai Kullum kuwa ko dare da rana Yana kururuwa dai. Ya tsatsage jikinsa kuwa Can kabari da duwatsu. 2) Ba wanda na da iko shi damre Mai ƙazamin Ruhun nan Sau da yawa ya tsutsunke Har sarƙoƙi ya karye su. 3) Sai ya iske Yesu na zuwa Daga nesa ya iske shi Ya sheƙo a guje domin Ya yi masa sujada fa. 4) Ya ce "ina ruwana da kai, Yesu kai Ɗan Allah ne ?" Ya ce "Ka fito daga cikin Mai ƙazamin Ruhun nan." 5) Ҡazamin ruhohin nan Sun shiga cikin gursunnai Su sun faɗi cikin teku Sun nutse dai, sun shaƙe kuwa. 6) Ta wurin ikon Maɗaukaki Yesu Ɗan Allah kaɗai Mai ƙazamin ruhun ya zama Mai hankali, mai shaida kuwa. 7) Sai mu bi Yesu don ya iya Cece mu daga Shaiɗan. Mu gaskanta shi Ɗan Allah ne Mai Cetonmu, Mai Kamnarmu.La Tua mano è sopra me 1000 рук ჩემი სულის მეფე Pán mi cestu dá جعان قلبي 神纪念我们 ạlrb rạʿy االامدا ەڭ جوعورقۇ ىسىم فى بيت لحم Того кто ранен был грехом
Song not available - connect to internet to try again?