1) Masoyina yana sama, shi ne Yesu Ɗan Allahnmu. Yana sama, yana shirya wurin zama can dominmu, saboda ni, ba ni da kowa, ko aboki a duniyan nan. Ruhunsa ne ya biɗa duk ya koya mana aikinsa. KORUS Masu-bi ku zo, mu bi Yesu Yesu shi ne makiyayi. (2x) Karatu: Ubanmu wanda ke cikin sama ---- (Addu'ar Ubangiji) 2) Ku ƴan ƙwaya ku shaida fa, Almasihu yana zuwa. Ku mutane, ku shaida fa Almasihu yana zuwa. Ku Pastoci, ku yi aniya, ku yi aiki da aminci. Ku je ku yi shaidar bishara, ku je ku kawo ƃatattu. Korus Karatu: Masoyina, masoyina yana sama. Shi ne Ɗan Allah wanda ya rnutu. Sabili da zunubanmu. Ƴanuwa Ku duba irin ƙauna da Yesu ya yi domin mu zama masu ƙaunar juna 3) Ku matasa, ku shaida fa Almasihu yana zuwa. Ku yara ma, ku shaida fa Almasmu yana zuwa. Zumuntar mata, ku yi aniya, Ku yi aiki da aminci, Ku je ku shaida bishara, Ku je ku kawo ƃatattu. Korus Karatu: Kamar yadda Yesu ya koya mana, ku ƴan ƙwaya, da masu shaidar bishara. da Pastoci, da su referan, da zumuntar mata, ku mutane duka, ku tashi tsaye, ku yi aikin Ubangiji fa, gama lokaci ya kusa, Yesu yana zuwa. Babu shakka zai ba kowa ladan aikinsa. Allah ya taimakemu. Amin.في سكون Amar iti era sufletul La tempesta non temere 耶稣的名大有权柄 Merhamet et yarattığın kullarına Uluslar Sevinsin РАБ'бимизин йолунда 영광 주님께 영광 Тагчг сө The fight is on
Song not available - connect to internet to try again?