1) Rana ta Ubangiji ta sake zuwa yau, Hutawa domin jiki, ranar sujada ma. A cikin taruwarmu, mun ta da muryarmu, Mun gode maka, Allah, domin hutawarmu. 2) A ranan nan mai tsarki, Yesu, mai fansarmu, na ikonsa ya tashi, ya gama cetonmu, Ya kwance sarkar Shaiɗan, ya tube ikonsa, Ta wurin mutuwarsa, ya ka da mutuwa. 3) A ranan nan mai tsarki, Mai Taimako ya zo A wurin Masu Binsa, ya zauna cikinsu. Ya ba su ikon shaida, ya kau da tsoro duk, Ya buɗe hankalinsu, ya cika zuciyarsu. 4) Mun gode maka, Allah, cikin alherinka, Ka tuna da ƴan Adam, ka ba su hutu ma. Ka taimake mu, Allah, mu tsare ranan nan Har ran da za mu gan ka a cikin Sama can.Naweka Dhambi Zangu Beytlehem ạgẖfr ly kl dẖnby Hospodinu podajme ruku Чьим словам поверишь ты? Sólo tengo tu Palabra Таң атканда ойгонуп, Сени чакырам Budem spievať Rab Gösterdi, - Rab Gösterdi قدني فأنت قائدي
Song not available - connect to internet to try again?