1) Ya ƙaunar Almasihu, Ban san iyaka ba, Da zurfinta da tsawonta Sun wuce faɗina. A gindin giciyen Almasihu Na zauna, hutun rai na yi. Rijiyar ƙauna cikakkiya da rai, Kai ka bayar a shayad da ni. 2) Ya ƙaunar Almasihu Wadda ta riƙe ni, Ta bi ni, ina nesa, Ta kawo ni wurinka. Ta amshi dukan zuciyata, Ta sa na zama bawanka. Duniya duk ta kasa jawo ni, Domin ikon ƙaunarka. 3) Ya ƙaunar Ubangiji, Ya zuciyar Allahnmu, Ga zunubi a duniya, Ga girman ƙaunarka. Ga ƙofar rai a buɗe yau, Ƙauna ta buɗe ta. Ba mu yin fahariyar kome, Sai dai giciyen Almasihu.ما أحلى السجود Głowo Kościoła, Zbawco nasz ليك مكان Isten Igéje gyorsan szalad yạ ʿạlm bḥạly Небесный дом оставил This Little Light of Mine يا جميع الأمم О мой Бог услышь Тебя молю я Žalm Veľkonočný
Song not available - connect to internet to try again?