1) Yesu Ubangijinmu ne, Jininsa ya saye mu, Daga hannunsa mun sami Ceto daga zunubi. Mu bayinsa, mu bayinsa, Sai mu yi ta aikinsa. 2) Almasihu ya fanshe mu, Ba da azurfa ba fa, Ba kuwa da zinariya ba, Sai da jininsa kaɗai. Mu bayinsa, mu bayinsa, Mu, hakika, nasa ne. 3) Ranmu duka ne ya saya, Rabin zuciya ba ya so. Shi ya ba da ransa duka, Namu duka ya ke so. Mu bayinsa, mu bayinsa, Kome namu za mu bayar. 4) Ga mutane cikin duniya, Ba su san Mai Ceto ba. Shi kuwa yana so su san shi Sai mu je mu neme su. Mu bayinsa, mu bayinsa, Sai mu je mu neme su. 5) Ƴanuwana, sai mu tuba, Sai mu yad da ƙyuyarmu, Ga mutane suna mutuwa, Sai mu ceci waɗansu Mu bayinsa, mu bayinsa, Ƙaƙa za mu ƙyale su? 6) Su da suka yi aniya, Masu yi da zuciya ɗaya, Ran da Yesu za ya komo, Za a ɗaukaka su dai. Bayin Yesu, bayin Yesu, Za su sami ladansu.حبك لي انت قادر Aide-nous à rebâtir ta maison الكلمة منك مش أوهام lmsẗ ạ̹ydyk Cum te-ai oprit de mult la han ياللي مليت حياتي أفراح 不可在路上停 yǎng wàng Зэв долыд, кор ми ставӧн ӧтвылысь
Song not available - connect to internet to try again?