1) Da tunawar ƙaunar Mai Ceto. Al'ajabi na ke yi. Ga Yesu ya sha wulakanci Don laifin da ni na yi. KORUS Al'ajabi! Al'ajabi! Wannan waƙa sai in yi. Al'ajabi! Al'ajabi! Mutuwarsa ta cece ni. 2) Dalilin jiƃinsa mai jini Da zafin addu'arsa Ba domin kansa ya yi ba, Sai domin zunubina. Korus 3) Mala'ika ya ji tausayinsa, Ya zo daga Sama can Domin ya ƙarfafa ransa A cikin wahalan nan. Korus 4) Ya ɗauke zunubai duka, Ya maishe su nasa ne. Ya kai su can bayan birni, Dominsu ya ba da rai. Korus 5) A can cikin daraja tasa Zan duba Mai Cetona. Zan rera waƙa gare shi Domin yawan ƙaunarsa. KorusRahmat Senga Iso Wielki dzień nadchodzi Смолкли на улицах звуки свирели În Ghetismani Isus În noapte-ngenuncheat Di Dalam Suka, Di Dalam Duka Pán Bůh pro mě má svůj plán Жить в свободе slạmk fạq ạlʿqwl Zastav se každý Любовь это все
Song not available - connect to internet to try again?