1) Sunan Yesu shi ne mafi ɗaukaka Cikin dukan sunaye. Babu wani suna wanda ya isa Cetonmu, sai shi kaɗai. KORUS Yesu ne Mai Ceto, Ba wani Allah za mu bi, Cikin sunansa, nasara, Babu shakka, za mu yi. 2) Yesu ya ci nasara da zunubi, Ba da ikon duniya ba, Sai ta wurin mutuwa da tashinsa Daga cikin kabari. Korus 3) Halin Almasihu mu ke so mu yi, Ruhunsa ya cika mu Don mu shaida shi ga dukan mutane, Cewa ya yi cetonsu. Korus 4) Sai mu ƙanƙantad da kanmu, ƴanuwa, Kamar yadda shi ya yi. Mu yi nufinsa da farar zuciya, Har matuka za mu bi. KorusCuán feliz la célica morada Сени менен болуу жакшы พระคุณพระเจ้า Дух Божий Среди нас сейчас داڭازالايت جانىم Ştie Domnul din ce noapte Доверяю я dwrt ktyr Как мне рассказать My Jesus, I Love Thee
Song not available - connect to internet to try again?